‘Isra'ila Babba’: Bayan Faduwar Assad, Isra'ila ta cigaba da Mamayar Yankunan Siriya

 


Bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad, Isra'ila ta ƙara ƙarfin hare-haren ta kan Siriya, ta ci gaba da ƙara mamayar ƙasar, har ta kai ga yankin da ta riga ta mamaye, wanda ya haɗa da Golan Heights, a wani mataki da ake ganin yana cikin shirin su na samar da"Isra'ila Babba".


A cikin wani mataki na Juyin mulki, ƙungiyoyin 'Yan Tawaye sun karbe birnin Damascus a ranar Lahadi, bayan makonni biyu na hare-harensu daga Aleppo, wanda ya kawo ƙarshen mulkin shekaru 20 na Bashar al-Assad.


Nan da nan bayan mayakan dake kiran kansu da Hayat Tahrir-al Sham sun karbe Damascus, Isra'ila ta kai hare-haren jiragen sama a fadin Siriya, ciki har da biranen Damascus, Homs, Tartous, Latakia, da Palmyra. Hakan ya kai ga rushe 80% na ƙarfin sojojin Siriya. 


A ranar Laraba, rundunar sojojin Isra'ila ta ce ta kai sama da hare-hare 480 kan makaman sojojin Siriya cikin sa'o'i 48 da suka gabata, ciki har da hare-hare kan jiragen ruwa, makaman yaki, da wuraren samar da makaman.


A lokaci guda, Isra'ila ta shiga yankin ƙofar Golan Heights, wanda aka ayyana a matsayin wuri ba tare da sojoji ba daga yarjejeniyar tsagaita wuta ta Majalisar Dinkin Duniya ta 1974. Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa Golan Heights zai kasance wani ɓangare na Isra'ila "har abada".


Wannan mataki yana daga cikin shirye-shiryen Isra'ila na faɗaɗa iyakokinta, wanda ke nuni da ƙoƙarin ɗaukar yankuna da aka saba ganin su a cikin tarihi na Isra'ila, ciki har da yankunan Siriya, Lebanon, Iraki, da Jordan.


Hukumar kasa da kasa, ciki har da ƙasashe kamar Iran, Qatar, da Iraki, sun yi suka kan wannan mataki na Isra'ila, suna ganin hakan a matsayin take hakkokin kasa da kasa.


Majalisar Dinkin Duniya ta kuma nuna rashin jin daɗin wannan matsayi, tana kiran shi da karya yarjejeniyar tsagaita wuta. Hakanan kuma, faɗaɗa wannan tsari na Isra'ila, tare da hare-harenta a Gaza da Lebanon, ya ƙara jefa yankin cikin tashin hankali.

Post a Comment

Previous Post Next Post