Ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu hukumomin Amurka da ke da alhakin murkushe zanga-zangar neman goyon bayan Falasdinawa da dalibai keyi da kuma take hakkokin bil'adama.
Iran ta kakabawa wasu jami'an Amurka 11 takunkumi, da suka hada da shugabannin 'yan sanda da kwamishinonin 'yan sanda, a karkashin wata doka ta 2017 da ke yaki da take hakkin bil'adama da ta'addanci.
Ana zargin wadannan mutane da murkushe zanga-zangar lumana da daliban jami'a da malaman jami'o'i da ke goyon bayan al'ummar Palasdinu suka yi na nuna adawa da ayyukan Isra'ila a Gaza. Takunkumin sun hada da:
- Toshe asusu da ma'amaloli a tsarin hada-hadar kudi na Iran
- Toshe dukiyoyin da ke cikin ikon Iran
- Haramta ba da biza da shiga Iran
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa an ƙaƙaba takunkumin ne domin mayar da martani ga mahukuntan Amurka da suke take hakkin bil'adama da kuma goyon bayansu ga laifukan da Isra'ila ke yi a Gaza. Ma'aikatar ta jaddada cewa za a aiwatar da takunkumin ne bisa ka'idoji da dokoki da suka dace.
Ana kallon wannan mataki na Iran a matsayin martani na diflomasiyya ga matakin da Amurka ta dauka, wanda Tehran ke kallonsa a matsayin cin zarafin bil adama da dokokin kasa da kasa. Takunkumin dai an ƙaƙaba shine da nufin dorawa mahukuntan Amurka alhakin ayyukansu, sannan kuma domin tallafawa al'ummar Palasdinu a fafutukar neman adalci da 'yanci.
