Ƙungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta Yemen ta bayyana gargaɗi kai tsaye ga Amurka da Isra’ila, tana cewa duk wani yunƙuri na kai hari ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran zai tayar da rikici a faɗin yankin Gabas ta Tsakiya.
Wani majiyar cikin Ansarullah ya shaida wa mujallar Newsweek ta Amurka cewa sojojin Yemen sun shiga matsayi na ƙarin shiri, kasancewar su a halin yanzu cikin yanayin yaƙi da Isra’ila, sakamakon hare-hare da kuma takunkumin da ake wa Gaza, wanda daga baya ya ƙara zuwa kan Yemen.
"Muna cikin cikakken shiri, kuma muna ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila,” in ji majiyar.
“Mun kai kololuwar shiri kan ko wane irin yuwuwar ɗagawa daga Amurka. Kuma duk wani hari kan Iran zai jawo yakin gabaɗaya a yankin.”
Majiyar ta kara da cewa Amurka ba ta da ikon kai hari ga kowace ƙasa a yankin don bauta wa muradun Isra’ila, tana mai cewa:
“Ba zai amfani al’ummar Amurka ba su tsunduma cikin sabon yaki don kare mulkin sahyoniyawa.”
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa a kwashe 'yan kasar Amurka daga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, domin “wuri ne mai hatsari.”
A wani bangare, Ministan Tsaron Iran, Janar Aziz Nasirzadeh, ya mayar da martani ga barazanar Amurka, yana mai cewa:
“Idan Amurka ta kai hari saboda faduwar tattaunawar nukiliya, Tehran za ta maida martani mai nauyi – ciki har da kai farmaki kan duk sansanonin sojin Amurka a yankin.”
Iran da Amurka sun sha tattaunawa sau biyar ta hanyar Oman dangane da shirye-shiryen nukiliya da cire takunkuman tattalin arziki daga kasar. Ana shirin gudanar da zagaye na shida a ranar Lahadi a Muscat.