Wani tsohon janar na HKI ya amince da cewa sojojin Isra'ila sun sha kashi sosai a yakin da suke yi a Gaza, ya kuma yi watsi da ikirarin da mahukuntan Isra'ila suka yi na raunana ko rusa kungiyar Hamas a matsayin kalaman siyasa kawai.
A cewar al-Mayadeen, kafar yada labaran Isra'ila ta rawaito cewa, tsohon Janar na Isra'ila Ishaq Brik ya amince da cewa ikirarin ci gaba da yaƙi domin raunanawa da kuma ruguza kungiyar Hamas, take ne kawai, maimakon manufa ta hakika ta soji.
Tsohon Janar din na Isra’ila ya amince da cewa, ‘Mun sha kashi sosai a yaƙin Gaza, yayin da sojojinmu kuma sun gaji sosai, sannan ga karancin harsasai, haka kuma rukunin injiniyoyinmu sun lalace sosai, mun yi asarar manyan ma'aikata, kayan aiki, da kayayyakin more rayuwa.'
Tsohon jami'in gwamnatin mamayar ya jaddada cewa sojojin ajiya kuma sun sanar da cewa ba za su gabatar da kansu domin a tura su yaki ba.
