Kungiyar Hizbullah ta Harba Makamai Masu Linzami Kan Isra'ila a Matsayin Martanin Kashe Kwamandanta

 


Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta kaddamar da hare-haren rokoki a wurare da dama na sojojin HKI a matsayin martani ga kisan da gwamnatin HKI ta yi wa daya daga cikin kwamandojinta a kudancin kasar Lebanon.


Kungiyar Hizbullah ta sanar da kai hare-haren ne a ranar Larabar, inda ta ce an kai hari da rokoki da dama kan sansanonin sojin Isra'ila guda biyar, ciki har da makaman Katyushas guda 100 da suka kai hari kan hedkwatar rundunar Golan da kuma na'urorin sojin sama da sojin makamai masu linzami na Isra'ila a sansanin Nafah.


Kungiyar ta bayyana cewa, hare-haren nata na mayar da martani ne ga harin da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai kan wata mota a kudancin Lebanon wanda ya shahadantar da babban kwamanda Muhammad Nimah Nasser, wanda aka fi sani da "Hajj Abu Naameh", tare da jikkata wasu da dama a safiyar ranar Laraba.


Wani mamba a kungiyar 'Loyalty to Resistance Bloc', bangaren siyasa na kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Lebanon, ya bayyana cewa kisan Abu Na'ameh ba zai sanyawa Hizbullah barazana ba, kuma kungiyar za ta ci gaba da tsayin daka wajen tinkarar ta.


Hassan Fadlallah ya jaddada cewa matakin da kungiyar Hizbullah za ta dauka na azabtarwa zai zo, kuma ya kamata makiya su gane cewa fafutukar gwagwarmaya ce ke da rinjaye.


 Abu Naameh shi ne kwamandan Hezbollah na uku da Isra'ila ta kashe tun farkon watan Oktoba lokacin da aka fara artabu tsakanin bangarorin biyu a yakin da gwamnatin kasar ke yi a Gaza.


Kisan nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar barkewar yaƙi tsakanin kungiyar Hizbullah da Isra’ila a ‘yan makonnin nan.


 Kungiyar gwagwarmayar Musuluncin ta gargadi Isra'ila game da kai irin wannan yaki, kuma ta ce a shirye take ta kare kasar Labanon.

Post a Comment

Previous Post Next Post