Ofishin siyasar ƙungiyar Ansarullah ta Yemen ya yi tir da shawarar Amurka na sanya su a jerin ƙungiyoyin ta'addanci.
A cikin sanarwar da suka fitar a ranar Alhamis, ƙungiyar ta bayyana wannan matsayin a matsayin ƙoƙari na rashin nasara domin hana Yemen ci gaba da goyon bayan ƙoƙarin adalci na Falasdinawa.
Ƙungiyar ta ce wannan shawara mara adalci na nufin ƙara tallafawa laifukan gwamnatin Sahyuniya kan al’ummar Falasɗin da kuma ƙara haifar da wahalhalu ga al’ummar Falasɗin.
Ansarullah ta zargi Amurka da kishiyar fili a kan al’ummar Yemen.
Sanarwar ta ce tarihin Amurka yana ɗauke da tabon ta’addanci kuma ba ta da damar sanya wasu ƙungiyoyi a matsayin 'yan ta’adda.
Ansarullah ta yi gargadi game da sakamakon wannan shawara kan harkokin tattalin arziki da na jin ƙai a Yemen da kuma ƙoƙarce-ƙoƙarce na zaman lafiya da suka kai ga ci gaba mai kyau.
A baya a ranar Alhamis, Nasr al-Din Amer, mataimakin shugaban sashen watsa labarai na Ansarullah, ya ce wannan ƙoƙarin da Amurka ta yi na sanya Ansarullah a matsayin ƙungiyar ta’addanci zai ci tura, kamar yadda ƙoƙarinsu na yaƙar ƙungiyar a teku ya ƙare da shan kaye.
“Zama a cikin jerin abokan Amurka shine haɗari mafi girma da kuma tayar da hankali fiye da sanya mu a matsayin ƙungiyar ta’addanci,” in ji shi.
Amer ya ƙara da cewa Amurka na kai hare-hare kan al’ummar Yemen saboda goyon bayansu akan Gaza, yana mai jaddada cewa wannan kiran da akewa ƙungiyar a matsayin 'yar ta’adda babbar girmamawa ce ga 'yan Yemen kuma muhimmin ɓangare ne na ci gaba da gwagwarmayarsu.
Ƙungiyar ta riga ta bayyana cewa ba ta da wani jari, asusun banki, ko kasuwanci a Amurka kuma membobinta ba sa tafiya wannan ƙasar (Amurka).