Shirun da Kasashen Turai Keyi ne Yasa Isra'ila ta Ƙara Girman kai

 


Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri a wata tattaunawa ta wayar tarho da babban jami'in diflomasiyyar kasar Austriya Alexander Schallenberg ya soki wasu gwamnatocin kasashen Turai da yin shiru da kuma rashin daukar mataki kan ayyukan ta'addanci na gwamnatin HKI.


A cewar Kamfanin dillancin labaran IRNA, Bagheri Kani ya tattauna da Schallenberg a daren jiya Talata game da ta'addancin gwamnatin sahyoniyawan da ya kai ga shahadar shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas a birnin Tehran a makon jiya.


"Abin takaicin shi ne, wasu kasashen Turai sun yi gum da bakinsu kan ayyukan ta'addancin gwamnatin sahyoniyawan da suka saba wa dokokin kasa da kasa, kuma hakan ya sa girman kan 'yan kungiyar masu aikata laifuka a birnin Tel Aviv ya kara tsananta wanda ya hakan ya ƙara tashin hankali da rashin tsaro a yankin." Yayin da yake ishara da kisan gillar da Isra'ila ta yi wa Haniyyah a Tehran wanda ya sabawa 'yancin kai da tsaron kasar Iran.


Ya kara da cewa: Bangaren Turai a zahiri sun toshe duk wata kafar diflomasiyya ta hanyar ƙin yin tir da ta'addancin da ake yi a fili tare da Amurka, har ma da hana kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa shugaban Hamas da kuma daukar duk wani mataki akan yahudawan sahyoniya.


Schallenberg ya bayyana damuwarsa game da tabarbarewar al'amura a yankin yammacin Asiya amma ya ci gaba da tsare manufofin kasarsa na rashin furta ko da kalma daya kan laifukan sahyoniyawan.  


 Yayin da yake kira ga dukkan bangarorin da su yi taka-tsantsan, babban jami'in diflomasiyyar na Austriya ya ce kasarsa na jaddada bukatar yin amfani da dukkan karfin diflomasiyya don rage tashe-tashen hankula.

Post a Comment

Previous Post Next Post