A ranar Laraba, mataimakin Admiral George M. Wikoff, kwamandan runduna ta 5 ta sojojin ruwan Amurka, ya amince cewa, duk da kokarin da Amurka ta yi, Amurka ta kasa dakile hare-haren da sojojin Yaman ke kaiwa kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya.
"Tabbas mun rage karfinsu, babu shakka a kan hakan, amma mun dakatar da su? A'a," in ji mai magana da yawun Cibiyar Dabaru da Nazarin kasa da kasa kamar yadda Jaridar Russia Today ta Naƙalto. Hare-haren baya-bayan nan kan jiragen ruwa na kasuwanci da sojojin Yaman suka kai, ya nuna cewa har yanzu sun kuduri aniyar kai hari kan jiragen ruwa a Gabas ta Tsakiya.
"Aikinmu shine mu rage karfinsu da kuma kiyaye tekun gurin tabbatar da shi cikin lafiya da kuma karkashin iko," in ji Wickoff. A cewarsa, rashin zaman lafiya a tekun Bahar Maliya da Tekun Aden na da nasaba da ayyukan 'yan kasar Yemen. "Za su iya dakatar da wannan a kowane lokaci."
Al'amurra sun ta'azzara a cikin tekun Bahar Maliya da Tekun Arabiya da kuma Tekun Aden tun bayan da sojojin Yaman suka fara kai hare-hare a watan Nuwamban da ya gabata kan jiragen ruwa na Isra'ila ko kuma wadanda ke da alaka da Isra'ila ko kuma suka nufi tashar jiragen ruwanta, a matsayin mayar da martani ga hare-haren da Isra'ila ta kaddamar kan Falasdinawa a Zirin Gaza.
A ranar 10 ga watan Oktoba ne sojojin kasar Yemen suka sanar da cewa za su goyi bayan bangarorin Falasdinawa a tunkarar sojojin Isra'ila a zirin Gaza da makaman roka da kuma hare haren sama "da sauran zabin soja" idan har Amurka ta tsoma baki ta hanyar soji a rikicin na Isra'ila da Falasdinu.
Sojojin Yamen dai sun gudanar da ayyuka da dama domin nuna goyon bayansu ga al'ummar Gazan tun farkon yakin da Isra'ila ta kaddamar a Gaza a farkon watan Oktoban da ya gabata, inda Yemen ɗin ta kai hare-hare a duk fadin yankunan Falasdinawa da aka mamaye, baya ga kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra'ila ko Jiragen ruwan da ke kan hanyar zuwa tashar jiragen ruwa a yankunan Falasdinawa da aka mamaye.
Ya zuwa yanzu dai hare-haren da Isra'ila ta kai a zirin Gaza ya yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa 39,677 galibi mata da kananan yara, yayin da wasu 91,645 suka jikkata.
Dakarun Yaman sun bayyana cewa ba za su daina kai hare-hare na ramuwar gayya ba.
Hare-haren nasu na teku ya tilastawa manyan kamfanonin sufurin jiragen ruwa da na Mai gurin dakatar da balaguro zuwa tashar jiragen ruwa na yahudawan sahyoniya.
