Iran Ta Tattauna da Jami'an Hamas Kan Harin da Isra'ila Takai a Wata Makaranta Dake Gaza

 


Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri Kani da mataimakin shugaban kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas Khalil Al-Hayya sun tattauna kan mummunan harin da Isra'ila ta kai kan wata makaranta a Gaza.


A wata tattaunawa ta wayar tarho, Bagheri Kani ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana yin kokari sosai wajen ganin kungiyoyin kasa da kasa da na yankin sun yi Allah wadai da sabon laifin da aka aikata.


A nasa bangaren jami'in na Hamas yayi ishara da kisan yara da mata da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke yi, inda ya bukaci kasashen duniya da su yi Allah wadai da wannan harin ta'addanci.


Ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da tuntubar Iran game da wannan batu.


Sama da Falasdinawa 100 ne aka kashe bayan wani kazamin harin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan wata makaranta a yankin Daraj a Gaza a daidai lokacin da ake gudanar da sallar asuba a ranar Asabar.

Post a Comment

Previous Post Next Post