Kungiyar Hizbullah ta Sake Harba Rokoki a Kan Yankunan Falasdinawa da Isra'ila ta Mamaye

 


Kungiyar gwagwarmayar Hezbullah ta kasar Labanon ta sake harba makaman roka da dama a wani harin ramuwar gayya da takai a Yankunan Falasdinawa da Yahudawan sahyuniya suka mamaye, in ji majiyoyin labarai.


Tashar talabijin ta Aljazeera ta ambato rahotannin kafafen yada labaran Isra'ila da ke cewa, an harba rokoki da dama a garin Miron da ke arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye a safiyar Laraba, inda tashar Channel 12 ta ce adadinsu ya kai 50.


Sakamakon harin, an yi ta jin karar Amsakuwwar nan ta Siren a matsugunan Yahudawan sahyoniyan da ke kusa da garin Miron, lamarin da ya zama na gargaɗi ga mazauna yankin.


Hare-haren dai ya biyo bayan sa'o'i kadan bayan da kungiyar Hizbullah ta jaddada goyon bayanta ga al'ummar Gaza tare da kai hari kan sansanin sojojin yahudawan sahyoniya da ke yankin Jal al-Deir da makamin roka.

Post a Comment

Previous Post Next Post