Shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana sa ran Iran za ta kauracewa shirin daukar fansa kan Isra'ila idan aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
A cewar IRNA, Biden, wanda ke cikin watannin karshe na wa'adin shugabancinsa na farko, ya yi ikirarin hakan a ranar Talata lokacin da aka tambaye shi ko tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da Hamas za ta iya hana kai harin Iran.
Sai yake cewa zai mayar da sauran lokacin da ya rage wajen samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Sannan kuma Za mu ga abin da za mu iya yi da kuma yadda Iran za ta mayar da martani. Ina sa ran idan aka tsagaita bude wuta a Gaza, Iran za ta fasa kaiwa Isra'ila hari, in ji shi yayin da yake mayar da martani kan tambayar da aka yi masa.
Ina cikin damuwa game da halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya wanda ya zama mai wahala, yana mai cewa: "Bari mu ga abin da Iran zata yi, za mu ga abin da zai faru idan aka kai hari."
Komai zaku iya cewa akan furucin wannan Shaiɗanin bawan, ku rubuta mana a Comment dake ƙasa.
