Falasdinawa 16 Ne Suka yi Shahada a Wani Sabon Harin Da Isra'ila Ta Kai a Gaza

 


Kafafen yada labaran Falasdinu sun bayyana cewa, an kashe Falasdinawa 16 a sabon hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin sahyoniyawa ta kai a yankin tsakiya da arewacin zirin Gaza.


Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Shehab ya ruwaito, Palasdinawa 7 da suka hada da kananan yara uku ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza.


Falasdinawa 4 da suka hada da kananan yara da dama kuma sun yi shahada a hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa wani gida da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Al-Maghazi da ke tsakiyar Gaza.


Wakilin Aljazeera ya rawaito cewa Falasdinawa 16 ne suka yi shahada a hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai a tsakiya da arewacin zirin Gaza a safiyar yau Laraba.


Tun a ranar 7 ga Oktoban 2023 gwamnatin Tel Aviv ta kaddamar da mummunan yaki a kan zirin Gaza, wanda ya yi sanadin Shahadar sama da mutane 39,929, tare da Jikkata sama da 92,000. 


Kana kuma an kuma yi sanadin ɓacewar Falasdinawa 10,000, da kuma tilastawa mazauna yankin da aka yi wa kawanya kusan miliyan biyu kauracewa gidajensu."

Post a Comment

Previous Post Next Post