Jagoran ‘yan adawar gwamnatin sahyoniya Yair Lapid ya yi gargadin cewa firaminista Benjamin Netanyahu da ministan kudi Bezalel Smotrich na kai gwamnatin kasar ga wani bala’in tattalin arziki.
"Ministan kudi da firaministan kasar duka sun fitar da sanarwa jiya inda suka bayyana cewa rage kimar lamuni na Isra'ila sakamakon yakin da ake yi ne," in ji Lapid a wani taron kungiyar Yesh Atid, inda ya kara da cewa, "Wannan karya ce. Dukkansu biyun karya suke yiwa jama'a."
Ya kara da cewa "Tuni a watan Yulin da ya gabata, watanni kafin a fara yaƙin, kamfanoni masu kima sun ba da hasashe mara kyau ga tattalin arzikin Isra'ila, kuma sun ce idan sakaci da rashin kula da tattalin arziki ya cigaba, darajar shi zata ragu," in ji shi.
Da yake kira ga Netanyahu da ya yi murabus nan take, ya ce idan ba tare da majalisar ministocin da za ta iya zartas da kasafin kudin da ya dace ba, darajar za ta ci gaba da raguwa.
Lapid ya kuma yi ishara da alkawarin da Iran ta yi na daukar fansa kan kisan da aka yi wa shugaban Hamas Ismail Haniyah a Tehran a ranar 31 ga watan Yuli, ya kuma ce matsalar tattalin arziki za ta hana Tel Aviv biyan bukatunta na tsaro da kuma dakile harin Iran.
