Kungiyar Hezbullah ta kasar Labanon ta ce ta kai hare-haren roka kan matsugunan Isra'ila dake Kiryat Shmona a arewacin Falasdinu da ta mamaye.
A cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta fitar a yammacin jiya Laraba ta ce mayakanta sun harba makaman roka na Katyusha a Kiryat Shmona a matsayin mayar da martani ga farmakin da yahudawan sahyuniya suka kai kan garin Abbasieh da ke kudancin kasar Lebanon, kamar yadda Kafofin yada labaran Lebanon suka ruwaito
Hakazalika jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun yi ruwan bama-bamai kan garuruwan Houla da Blida da ke kudancin kasar Lebanon, cibiyar labarai ta Al Mayadeen da ke birnin Beirut ce ta ruwaito.
Tun bayan farmakin da dakarun gwagwarmayar Falasdinawa suka yi na Guguwar Al-Aqsa, kungiyar Hizbullah ta ci gaba da kai hare-hare na ramuwar gayya a kowace rana a kan wuraren da Isra'ila ta ke, domin yin artabu da sojojin yahudawan sahyuniya a arewacin kasar Falasdinu, da kuma kawar da wasu daga cikin matsin lamba daga kan 'yan maƙawama a Gaza.
Dakarun Kungiyar Hezbullah sun lalata sansanonin sojin Isra'ila da dama, da kuma kayan aikin soji kamar tankokin yaki, da motocin daukar ma'aikata, da kuma motocin masu sulke.
