Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya ba da rahoton mutuwar kananan yara Falasdinawa 1,000 marasa lafiya da kuma jikkata sakamakon rufe hanyar Rafah da Masar a cikin kwanaki 100 da suka gabata.
"Bayan cinna wuta, lalata mashigar Rafah, sojojin Isra'ila sun rufe wannan mashigar ta Falasdinu da Masar sama da watanni uku, kamar yadda ofishin gwamnatin Gaza ya sanar a cikin wata sanarwa da IRNA ta rawaito a daren Laraba.
Ofishin ya damu matuka da yadda ayyukan da sojojin yahudawan sahyoniya suke yi a Gaza ya haifar da karuwar wahalhalu ga bil'adama. Waɗannan ayyukan haramun ne kuma sun saba wa dokokin ƙasa da ƙasa da haƙƙin ɗan adam. Suna kuma keta yarjejeniyoyin duniya. Wannan lamari ne mai tsananin gaske da ke bukatar kulawa da daukar matakai don dakile barnar da ake yi a Gaza.
Haramtacciyar Gwamnatin na ci gaba da hana shigo da kayayyaki iri-iri zuwa zirin Gaza da suka hada da kayayyakin jinya, kuma hakan na nuni da aniyar gwamnatin sahyoniyawan na lalata bangaren kiwon lafiya saboda rashin magunguna da kayan aiki na iya tilasta rufe wasu asibitocin da suka rage.
Ofishin yada labarai na Gaza ya kuma sanar da cewa a cikin wannan lokaci gwamnatin sahyoniyawan ta hana mutane 25,000 marasa lafiya da wadanda suka jikkata fita kasashen waje domin neman magani, sakamakon haka sama da yara 1,000 da majiyyata da kuma wadanda suka jikkata suka rasa rayukansu.
Ta bukaci al'ummomin kasa da kasa da dukkan hukumomi da su yi Allah wadai da laifukan tare da dora wa gwamnatin sahyoniyawa da Amurka alhakin hatsarin da ke tattare da rufe mashigar Rafah da hana shigo da kayayyakin kiwon lafiya da kayan agaji zuwa Gaza."
Muna roqon Allah daya ba Al'ummar Falasdinu mafita, ya tarwatsa Isra'ila da magoya bayan ta baki daya.
