A cewar jaridar Wall Street, gwamnatin Biden na shirin aika bama-bamai na sama da dalar Amurka miliyan 750 zuwa Saudiyya a cikin watanni masu zuwa.
Jaridar ta bayyana gagarumin sauyi a alakar Amurka da Saudiyya.
Fadar White House ta yanke shawarar dawo da aika makamai zuwa Saudiyya don inganta dangantakar da ke tsakaninsu da cimma manyan manufofi guda biyu kamar haka:
- Na farko cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza
- Na Biyu Taimakawa Saudiyya da Isra'ila su daidaita dangantakarsu.
A cewar su sun ɗauki wannan matakin ne da nufin karfafa alaka da Saudiyya, da kuma samar da zaman lafiya a yankin.
Jaridar Wall Street ta ruwaito cewa, matakin cigaba da shigo da wadannan kayayyaki na nuni da kokarin da fadar White House ke yi na karfafa alaka da Riyadh, da nufin ci gaba da tsagaita bude wuta a zirin Gaza da kuma samar da damar daidaita yarjejeniya tsakanin Saudiyya da Isra'ila.
Matakin dai ya biyo bayan tabarbarewar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tsawon shekaru. Biden, wanda da farko ya yi alkawarin daukar kasar Saudiyya a matsayin saniyar ware, saboda yadda take hakkin dan Adam da kuma kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Khashoggi, a hankali ya sassauta matsayinsa, musamman bayan ziyarar da ya kai Saudiyya a shekarar 2022.
Dana Stroul, tsohon jami'in Pentagon, ya ce Saudi Arabiya za ta dauki wannan shawarar a matsayin hanyar gyara babbar matsala a dangantakarsu da Amurka. Har ila yau, Amurka tana ba wa Saudiyya tukwici don taimaka wa tsaron yankin da kuma kasancewa a shirye don yin sulhu da Isra'ila.
Saudi Arabia na daya daga cikin manyan masu shigo da makamai a duniya, a cewar Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya ta Stockholm (SIPRI).
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama kamar Amnesty International sukan yi suka ga Amurka kan sayar da makamai ga Saudiyya. Suna masu cewa ana amfani da wasu daga cikin wadannan makaman ne akan kasar Yaman.
Bayan kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Khashoggi a shekarar 2018, wanda hukumomin leken asirin Amurka suka alakanta da Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, Jamus ta sanar da sanya takunkumin sayar da makamai ga Riyadh, wanda ta dage a watan Janairu.
Source: Almasirah English
