Hamas: Dole Ne Tsagaita Wuta Ya Ƙunshi Cikakkiyar Janyewar Isra'ila Daga Gaza

 

Kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas ta sake jaddada cewa duk wata yarjejeniya da Isra'ila dole ne ta tabbatar da tsagaita bude wuta a Gaza, da janyewar sojojin Isra'ila gaba daya da kuma yarjejeniyar musayar fursunoni.


Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Alhamis ta ce, kamata ya yi yarjejeniyar ta sauwaƙa wajen dawo da Falasdinawa da suka rasa matsugunansu, da kuma sake gina yankunan da aka lalata. 

 Kungiyar Hamas ta na kallon tattaunawar da ake yi a Doha dangane da tsagaita bude wuta da musayar fursunoni daga mahangar dabaru da nufin kawo karshen hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, in ji wani jami'in Hamas Hossam Badran a cikin sanarwar. 

Badran ya kara da cewa "Hamas ta yi imanin cewa duk wata tattaunawa dole ne ta kasance bisa tsarin da aka amince dashi a baya. Abin da ke hana cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza shi ne ci gaba da kaucewar 'Isra'ila'." 

"Duk wata yarjejeniya dole ne a cimma cikakkiyar tsagaita bude wuta, da ficewar (Isra'ila) gaba daya daga Gaza, (da) dawo da 'yan gudun hijira, tare da yarjejeniyar musayar fursunoni," in ji shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post