Da take tsokaci kan tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza da ake yi a Qatar, Iran ta yi gargadi game da "ha'inci da rashin gaskiya" na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da babbar mai goyon bayanta, Amurka.
Ministan harkokin wajen Iran na rikon kwarya Ali Bagheri Kani ya yi wannan gargadin a wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaminista kuma Ministan Harkokin Wajen Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani a ranar Juma'a. Wannan ita ce hirarsu ta biyu cikin sa'o'i 24.
Kani ya rubuta a cikin wani sako da aka buga a dandalin sada zumunta na X a yammacin ranar Juma'a cewa, shi da firaministan Qatar sun yi musayar ra'ayi game da ci gaban tattaunawar kwana na biyu na dakatar da kisan kiyashin da 'yan sahayoniya ke yi a Gaza.
Ya kara da cewa, "Da yake magana kan zalunci da aikata laifukan sahyoniyawan a Gaza, na yi gargadi game da ha'inci da rashin gaskiya na kungiyar masu aikata laifuka da ke mulkin Tel Aviv da kuma babbar mai goyon bayansu, Amurka, a kan teburin tattaunawa," in ji shi.
Tun da farko dai kasashen Amurka da Qatar da Masar sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka ce sun gudanar da tattaunawar tsagaita bude wuta a zirin Gaza cikin yanayi mai kyau a Doha babban birnin kasar Qatar. Sun kara da cewa tattaunawar ta kasance "mai mahimmanci, kuma mai ma'ana."
Masu shiga tsakani sun gabatar da wasu "shawarwari" wanda zai ba da damar saurin aiwatar da yarjejeniyar da za ta kawo karshen yakin Gaza da kuma ganin an saki fursunonin Isra'ila, in ji sanarwar hadin gwiwa.
Masu shiga tsakanin su uku sun yi iƙirarin cewa shawarar tasu "zata rage giɓin da ke tsakanin bangarorin,” suna nufin Hamas da kuma Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Sabbin sharuɗɗan da aka bayyana a cikin Tattaunawar, sun haɗa da yadda gwamnatin Isra'ila zata cigaba da aje sojojinta a cikin Gaza a iyakar bakin teku da Masar, in ji hukumar, cewar wata majiya mai tushe.
Sai dai rahotanni sun ce Hamas ta ce ba za ta amince da sabbin sharudda daga gwamnatin Isra'ila ba kamar yadda sabuwar shawara ta bayyana.
Kani ya ce Amurka na ba da makamai ga Isra'ila wanda hakan ya sa ta zama "mai hadin kai, ba mai shiga tsakani ba."
"Don haka na jaddada yin amfani da dukkan karfin iko wajen tilasta wa 'yan ta'addar sahyoniyawan su daina kashe-kashe da laifuka a Gaza," in ji shi.
Duk da tattaunawar tsagaita bude wuta da aka yi, gwamnatin Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare ta sama da na bindigogi a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya a daidai lokacin da yakin kisan kare dangi ya shiga wata na goma sha daya.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da yaƙin har sai abin da ya kira "kawar da" Hamas, al'amarin da kungiyar da ma wasu jami'an Isra'ila da kawayen ta suka ce ba zai yiwu ba.
Kisan gilla na baya-bayan nan ya kai adadin Falasdinawa da aka kashe zuwa sama da 40,000 tare da jikkata wasu fiye da 92,400.
