Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar da sake kai wani hari da jiragen yaki marasa matuka a kan sansanin sojin HKI da ke arewacin kasar Falasdinu da ta mamaye.
A cewar rahoton na tashar talabijin ta Al-Manar, A cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta fitar a jiya litinin da Dare ta sanar da cewa, harin da Jirgin yaki mara matuki yakai kan sansanin na Niriya martani ne ga hare-haren da HKI suka kai a yankin Mis al-Jabal da ke kudancin kasar Labanon tare da nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu.
Tun da farko dai, an yi ta jin karar Na'urorin gargadi a wasu matsugunan Isra'ila da ke arewacin yankunan Falasdinawa da aka mamaye, sakamakon wani harin da aka kai da jirgi mara matuki.
Tashar talabijin ta Channel 13 ta bayar da rahoton cewa, an harba jirage marasa matuƙa guda takwas zuwa yankunan da aka mamaye daga kasar Lebanon a cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
A daren Lahadin da ta gabata, kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa, an kaddamar da wani jerin gwanon jiragen yakin kunar bakin wake a hedkwatar sabuwar runduna ta 91 ta Elite Barracks, inda suka kai hari a wuraren da jami'anta da sojojin suke, inda suka yi musu luguden wuta kai tsaye tare da haddasa asarar rayuka da dama. raunuka a kansu.
Kafofin yada labaran yahudawan sahyoniya sun kuma bayar da rahoton cewa, an samu hasarar rayuka da dama sakamakon fashewar wani jirgi mara matuki a yankin Ayelet Hashahar a daren Lahadi.
