An kai hari kan sansanin sojin sama na Ain al-Asad na Amurka da ke yammacin Iraki sau biyu da rokoki a cikin dare, lamarin da ya Jikkata dakaru da dama, yayin da daya daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali.
Tun da farko dai mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka ya tabbatar da samun waɗanda suka Jikkata a harin na farko da ake kyautata zaton na makamin roka ne da aka kai sansanin da yammacin ranar Litinin.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, an harba makaman roka na Katyusha guda biyu a sansanin Ain al-Asad. Daga baya an ruwaito cewa akalla sojojin Amurka biyar sun jikkata, kuma yanayin daya daga cikin wadanda suka jikkata ya munana.
Wasu kafafen yada labarai na Amurka sun ambato kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon na cewa an jikkata wasu sojojin Amurka da ke sansanin.
"Alamomin farko sun nuna cewa jami'an Amurka da dama sun jikkata," in ji kakakin, ya kara da cewa ba a san cikakken adadin wadanda suka jikkata da kuma adadin wadanda abin ya shafa ba a halin yanzu.
Sai dai wasu kafafen yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun bayar da rahoton mutuwar sojojin Amurka 2 a harin.
Cibiyar sadarwa ta Al-Mayadeen ta Lebanon, ta ruwaito cewa, an ji karar fashewar abubuwa har guda uku da makamin roka da kuma Jirage marasa matuka a sansanin Ain al-Assad.
'Yan sa'o'i kadan bayan haka, a safiyar ranar Talata, majiyoyin labarai sun ba da sanarwar sake kai wani hari kan Ain al-Asad amma ba su bayar da cikakken bayani kan sabbin hasarar rayuka ko barna ba.
Rahotanni sun ce an sake kai hari sansanin ne a daidai lokacin da wani jirgin soji ke tashi domin jigilar sojoji da suka samu raunuka daga can.
