Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi ikirarin cewa, domin rage zaman dar-dar a yankin yammacin Asiya da kuma kare gwamnatin Isra'ila, ta ba da umarnin tura karin Jiragen yaki na Sama dana Ruwa a yankunan da ke karkashin ikon sojojin Amurka da na Turai.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar ranar Asabar, kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, Sabrina Singh, ta ce Sakatare Lloyd Austin, ya ba da umarnin yin gyare-gyare ga matsayin Sojojin Amurka don bada tsaro ga Sojojin na Amurka, da kara ba da taimako ga tsaron Isra'ila, da kuma tabbatar da cewa Amurka a shirye take ta mayar da martani ga duk abinda zai iya faruwa."
Kakakin ta kuma yi nuni da cikakkun bayanai game da canje-canjen, tana mai cewa, "Don ci gaba da kasancewar sojojin ruwa masu ƙarfi a Gabas ta Tsakiya, Sakataren ya umarci USS Abraham Lincoln Carrier Strike Group da ya maye gurbin USS Theodore Roosevelt Carrier Strike Group".
Sakatare Austin ya tura da karin jiragen ruwa na yaki wadanda za su iya bada kariya daga makamai masu linzami zuwa Turai da Gabas ta Tsakiya. Har ila yau, Amurka tana shirye-shiryen tura na'urorin kariya daga makamai masu linzami na ƙasa."
"Sakataren ya kuma ba da umarnin tura karin tawagar Jiragen Yaƙi zuwa Gabas ta Tsakiya, domin karfafa karfin jiragen sama," in ji ta.
Jami'an Amurka sun fada a Jiya Juma'a cewa Washington a shirye take ta tura da karin jiragen yaki zuwa yankin domin mayar da martani ga barazanar Iran da kungiyoyin gwagwarmaya a Gaza, Lebanon da kuma Yemen, wadanda ke son kai wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila hari a cikin 'yan kwanaki masu zuwa a matsayin ramuwar gayya kan kisan da aka yi wa Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na Hamas.
Haniyeh ya yi shahada ne a safiyar ranar Laraba, a lokacin da yake birnin Tehran don halartar bikin rantsar da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian.
