An bayar da rahoton cewa, an kai wani mummunan hari ta yanar gizo a shafukan intanet na filayen jiragen saman Isra'ila.
A cewar Al Mayadeen, Kafofin yada labaran Isra'ila sun bayar da rahoton cewa, bayan wannan mummunan harin ta yanar gizo, shafin yanar gizon tashar jirgin sama na Ben Gurion da ke Tel Aviv shi ma an kasa shigar shi.
Don haka, an soke tashin jirage da dama na gwamnatin Sahayoniya.
Tashar Channel 12 ta sahyoniya ta tabbatar da cewa shafin yanar gizon tashar jirgin sama na Ben Gurion da ke birnin Tel Aviv ya sauka, suna iƙirarin cewa hakan ya faru ne sakamakon rububin da masu ziyartar shafin suke yi.
Ko menene ra'ayin ku akan hakan, ku rubuta mana a comment section dake ƙasa.
Tags
Isra'ila
