Siriya Za Ta 'Yantu: Kwamandan IRGC Ya Maimaita Maganar Jagora

 


Babban Kwamandan Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Manjo Janar Hossein Salami, ya sake nanata hasashen Ayatollah Seyyed Ali Khamenei cewa matasan Siriya za su 'yanto kasarsu daga mamaya.


Da yake magana a Tehran a ranar Lahadi, Janar Salami ya kwatanta ikon kasashen waje a Siriya da “karnuka masu yunwa” da suke lalata kasar. Ya ce Sahayoniyawa suna aiki a kudu yayin da wasu ke mamaye arewa da gabashin kasar.


Ya nuna cewa ikon Sahayoniyawa na Leken Asiri kan iyalai a Damascus abinƙi ne, yana mai jaddada bukatar matasan Siriya su taso su yi tawaye.


Haka ma Ayatollah Khamenei ya jaddada cewa dakarun kasashen waje, ciki har da Amurka, za su fice daga Siriya ne kawai ta hanyar dagewar masu adawa.


Manjo Janar Salami ya kara gargadi cewa Sahayoniyawa za su biya farashi mai tsada kan ayyukansu kuma za'a yi Nasara akan su a yankin.


Masu ba da shawara na sojin Iran sun kasance a Siriya ne don kare martaba, ba don neman mamaya ko cika burace-burace ba.


Tun a shekarar 2011, Iran ta tallafa wa Siriya kan tashe-tashen hankula da kasashen waje ke daukar nauyinsu, wanda ya kai ga nasara babba kan Daesh a shekarar 2017.


Duk da haka, yankunan arewacin Siriya sun kasance karkashin 'yan tawaye dake dauke da makamai, yayin da Isra’ila ke cin gajiyar halin da ake ciki don fadada mamayarta.

Post a Comment

Previous Post Next Post