Isra’ila Ta Kai Sama da Hare-hare 800 Akan Syria Tun Bayan Faduwar Assad

 


Dakarun Isra’ila sun kai hare-hare fiye da 60 akan Syria cikin sa’o’i 12, wanda ya sa adadin hare-haren ya kai kusan 800 cikin mako guda.


Hare-haren na Isra’ila sun fi mayar da hankali ne kan birnin Damascus da kewayenta, inda suka lalata wuraren ajiye makamai da tsarin kariyar sararin samaniya.


Hare-haren sun kuma shafi wuraren ajiye makamai a lardin Deraa a kudancin kasar da kuma Homs da ke tazarar kilomita 80 daga arewacin Damascus.


Haka kuma Tankunan Isra’ila da motocin yaki sun kutsa cikin garuruwa da dama a lardin Quneitra na kudu maso yammacin Syria, yayinda suke lalata hanyoyi, cibiyoyin ruwan sha, da layukan wutar lantarki.


Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare akan Syria, inda hare-haren suka kara tsananta bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad a Damascus.


Hare-haren baya-bayan nan sun biyo bayan jawabin ministan yaki na Isra’ila, Israel Katz, wanda ya ce dakarunsu da suka kwace yankin Golan Heights daga Syria za su ci gaba da zama a kan tsaunin Hermon har lokacin hunturu.


Dakarun Isra’ila sun kutsa cikin wani yanki marar makamai (demilitarized zone) a Syria bayan ƙungiyar HTS da ta ke da alaƙa da al-Qaeda ta kwace iko da ƙasar a makon da ya gabata.


Abu Mohammed al-Jolani, jagoran HTS, ya taba cewa Damascus ba za ta shiga rikici da Tel Aviv ba.


Sai dai yanzu Jolani ya soki hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa Syria, yana mai cewa hujjojin da suke bayarwa ba su da ƙarfi.


Ya kara da cewa Isra’ila tana amfani da ƙaryar hujjoji don ganin ta halatta hare-harenta akan Syria.


Kasashen yankin sun roƙi ‘yan Siriya su yi aiki don gujewa shiga cikin rikice-rikice bayan da HTS ta kwace iko da birnin Damascus.

Post a Comment

Previous Post Next Post