Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya bayyana cewa “ba abu ne marar yiwuwa ba” a Yankewa Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Hukuncin Kisa saboda laifukan yaki da ya aikata kan Falasdinawa a Gaza.
Gharibabadi ya bayyana a wata hira cewa duk da Kotun Hukunta Laifukan Yaki (ICC) ta bayar da takardar kama Netanyahu da wasu jami’ansa, matakin nata ya taƙaita. Ya bada shawarar cewa kasashen da ke goyon bayan Falasdinawa za su iya kafa kotu ta hadin gwiwa don yanke hukuncin kisa ga wadannan Laifuka.
Ya jaddada muhimmancin aiwatar da irin wannan hukunci, inda ya yi nuni da kokarin da Afirka ta Kudu da wasu kasashe ke yi a Kotun Duniya (ICJ) don tabbatar da Isra’ila ta amsa laifinta na kisan kiyashi.
Ya kuma zargi Amurka da hannu a laifukan Isra’ila, yayinda take bayar da tallafin soja, siyasa, da diflomasiyya. Ya ce Isra’ila ba za ta iya Rayuwa ba ba tare da goyon bayan Amurka ba.
