Mazauna Isra’ila Da Dama Sun Ji Rauni Bayan Harin Makami Mai Linzami daga Yemen

 


Wasu mazauna Isra’ila sun ji rauni bayan makami mai linzami da aka harba daga Yemen ya nufi wurare muhimmai a tsakiyar yankunan da Isra’ila ta mamaye, wanda ya haifar da kararrawar gargadi.


A cewar tashar Isra'ila Channel 14, wasu mazauna sun ji rauni a yayin da suke neman mafaka. Kararrawar Sirens tayi qara a Tel Aviv da wasu garuruwa a cikin yankunan da aka mamaye.


Sojojin Isra’ila sun bayyana cewa na’urorin kariyar su sun dakile makamin mai linzami kafin ya shiga sararin samaniyar yankunan da aka mamaye.


Janar Yahya Saree, kakakin rundunar sojin Yemen, ya bayyana cewa makamin mai linzami mai suna “Palestine 2” ne aka yi amfani da shi wajen kai harin kan Tel Aviv, domin nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza.


Saree ya yi gargadi cewa sojojin Yemen za su ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin Isra’ila har sai an dakatar da hare-haren Gaza kuma an dage takunkumi.


Sojojin Yemen sun kai hare-hare kan Tel Aviv da Ashkelon, inda suka tsallake kariyar sararin samaniyar Isra’ila. A lokaci guda, sun jaddada goyon bayansu ga Falasdinawa kan mamayar Isra’ila.


Kungiyar gwagwarmaya ta Yemen ta yi alkawarin ci gaba da hare-hare har sai Isra’ila ta dakatar da yaki a Gaza. Har wala yau Sojojin Yemen din kuma suna kai hari kan jiragen ruwa da ke goyon bayan Isra’ila don tilasta ta dakatar da kisan kiyashi a Gaza.

Post a Comment

Previous Post Next Post