Ministan Harkokin Wajen Ireland, Micheal Martin, ya ce neman a ɗauki mataki kan kisan kare dangin da Isra’ila ke yi a Gaza da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa ba "Ayyukan nuna kiyayya bane ga Isra’ila."
Yayin da yake magana da manema labarai kafin taron ministocin harkokin wajen EU a Brussels, Martin ya kare matsayin Ireland bayan Isra’ila ta yanke shawarar rufe ofishin jakadancinta a Dublin, tana zargin Ireland da "matsananciyar kiyayya ga Isra’ila."
"Ireland ta tsaya kan matsayinta na neman a ɗauki mataki kan abin da ke faruwa a Gaza tare da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa da haƙƙin ɗan adam," in ji Martin.
Jakadan Ireland ya jaddada cewa Ireland tana ci gaba da kira da a gaggauta tsagaita wuta, a saki dukkan fursunoni, kuma a ƙara kai agajin jin kai zuwa Gaza.
Martin ya kara da cewa amincewa da ƙasar Falasɗinu ba ya nufin kiyayya kuma bai kamata a gan shi a haka ba.
Ya sake jaddada goyon bayan Dublin ga amfani da kotunan ƙasa da ƙasa, kamar ICJ da ICC, don ɗaukar mataki kan laifukan yaƙin Isra’ila a Gaza.
Firayim Ministan Ireland, Simon Harris, ya bayyana rufe ofishin jakadancin a matsayin dabara daga Isra’ila don kauce wa magana kan abin da take aikatawa a Gaza da Yammacin Kogin Jordan.
Harris ya yi Allah-wadai da ayyukan Firayim Ministan Isra’ila, Netanyahu, yana mai kiran su da "abin kyama," tare da cewa Ireland bazata taɓa yin shiru Akan suba.
Ireland, tare da Spain da Norway, za su ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen amincewa da Falasɗinu duk da adawa daga Isra’ila.
