Matsananciyar Matsin Lambar Trump Kan Iran Baza tayi Aiki ba: Masani

 


Wani masani ya bayyana cewa Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump, ba zai yi nasarar dawo da shirinsa na matsin lamba kan Iran ba idan ya koma ofis a ƙarshen Janairu.


A cewar Durso a Article ɗin shi The Hill, halin da Iran ke ciki a yau ya sha bamban da wanda ta tsinci kanta a 2018 lokacin da Trump ya ƙaddamar da manufofin tsauraran matakai. Ya jaddada cewa duk da takunkumin Amurka, Iran ta ƙara ƙarfi a ɓangaren siyasa da tattalin arziki.


Masanin ya nuna yadda Iran ke inganta dangantakarta da ƙasashen yankin irin su Saudiyya, Qatar, da UAE, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da Rasha da China. Wannan, a cewarsa, ya rage tasirin sake aiwatar da wannan tsari.


Ya kuma bayyana yadda Iran ta yi nasara wajen gujewa tasirin takunkumi ta hanyar ƙara yawan jiragen ruwan mai da take fitarwa tun daga daga shekarar 2021 zuwa yanzu. Durso ya ce ba za a iya dakatar da fitar da man Iran ba, ko da Trump ya sake kakabawa ƙasar takunkumi.


A ƙarshe, Durso ya ce gwamnatin Iran a yanzu ta nuna shirinta na yin hulɗa ta diflomasiyya, kuma akwai yiyuwar Trump da tawagarsa za su nemi tattaunawa kafin watan Oktoba na 2025, lokacin da dokokin takunkumi kan Iran za su ƙare dindindin.

Post a Comment

Previous Post Next Post