Akalla mutane 20 sun jikkata bayan makami daga Yemen ya fada Tel Aviv

 


Akalla mutane 20 mazauna Haramtacciyar Ƙasar Isra’ila sun jikkata bayan wani makami mai linzami da aka harba daga Yemen ya fada tsakiyar yankunan da Isra’ila ta mamaye na Falasɗinawa. 


Jaridar Ha’aretz ta ruwaito cewa an kai waɗanda suka jikkata zuwa cibiyar lafiya ta Wolfson da ke Holon da kuma asibitin Ichilov a Tel Aviv.


Makamin ya haifar da kararrawar Sirens a daidai 3:44 na dare, wanda ya sa miliyoyin mutane suka yi gaggawar shiga mafaka. Sojojin Isra’ila sun amince da gazawar tsarin kariyar sararin samaniyar su, wanda yasa suka fara bincike.


Harin makamin ya faru ne kwana biyu bayan dakarun Yemen sun kai hari kan wuraren sojojin Isra’ila biyu a Tel Aviv, yayinda sukayi amfani da makamai masu linzami na ballistic mai suna Palestine-2. Sai ita kuma Isra’ila ta mayar da martani ta hanyar kai hare-haren sama kan wuraren makamashi da tashar jiragen ruwa a Yemen.


Dakarun Yemen sun bayyana cewa ba za su daina hare-harensu ba har sai Isra’ila ta daina kai hare-hare a Gaza. 'Yan Yemen sun nuna cikakken goyon bayansu ga Falasdinawa tun bayan da rikicin ya ƙara kamari ranar 7 ga Oktoba, 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post