Seyed Davoud Bitaraf, wani ma’aikacin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus, ya rasa ransa sakamakon harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai a ranar 15 ga Disamba, 2024.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yi Allah wadai da kisan, ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga dangin marigayin da al’ummar Iran. Ya bayyana cewa an gano gawar Bitaraf kuma an dawo da ita Iran.
Baghaei ya jaddada cewa gwamnatin rikon kwarya ta Syria tana da alhakin gano wadanda aikata laifin tare da hukunta su, yana mai cewa ana ci gaba da bibiyar lamarin ta hanyoyin diflomasiyya.
Jakadan Iran a Syria ya bayyana cewa ofishin jakadancin Iran da ke Damascus zai koma aiki da zarar an tabbatar da tsaron ma’aikatan.
Da yake jawabi a taron manema labarai, Baghaei ya bayyana cewa tsaron ma’aikatan yana daga cikin abubuwan da suka fi muhimmanci, kuma ana ci gaba da tsare-tsare don hakan.
Ya tabbatar da cewa Iran za ta bude ofishin da zaran abubuwa sun inganta.
