Amurka Ta Kama Wasu Mutanen Iran Don Samun Bayanan Sirri

An kama wasu 'yan Iran guda biyu a Amurka da Italiya bisa zargin samar da kayan aiki ga jiragen sama marasa matuka da ake zargin sun yi amfani da su wajen kai hare-hare kan sojojin Amurka—wanda Iran ta musanta da cewa zargi ne marar tushe.

A ranar 16 ga Disamba, 'yan sandan Italiya sun kama Mohammad Abedini Najafabadi, mai shekaru 38, a filin jirgin saman Milan yayin da yake shirin tafiya Switzerland. Kama shi, wanda aka yi bisa bukatar Amurka, ya katse duk wata hulda da shi kai tsaye.

Hakazalika, an kama Mahdi Mohammadsadeghi, mai shekaru 42, wanda mazaunin Amurka ne, a Massachusetts a kusan wannan lokaci.

An danganta kamen da wani harin jiragen sama marasa matuka da aka kai a ranar 28 ga Janairu kan sansanin sojojin Amurka a Jordan, inda aka kashe sojoji uku da jikkata wasu 47.

FBI ta yi ikirarin cewa kayan aikin da aka yi amfani da su a harin an samo su ne daga hannun mutanen da aka kama.

Wani abokin aiki na Abedini ya bayyana cewa shi dan asalin Iran ne kuma Shugaban Kamfanin SDRA, wanda ke samar da kayan aune-aune tare da kayan amfani a fannoni daban-daban wadanda doka ta amince dasu, ciki har da na lafiya da wasanni.

Gwamnatin Amurka ta kirkiri zarge-zarge, tana ikirarin cewa an yi amfani da wadannan kayan aiki a cikin jirage marasa matuka da aka kai hare-haren, wanda ya kai ga kamawa da gurfanar da su a gaban shari'a.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran tana kokarin ganin an sako Abedini ko a samu damar tuntubarsa kafin a dauki wani matakin shari’a.

Post a Comment

Previous Post Next Post