Hamas: Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Sakamakon Juriya da Gwagwarmaya a Gaza Tsawon Watanni 15

Palasdinawa sun yi murna a Gaza ranar 15 ga Janairu, 2025, suna daga tutar ƙasa bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniya ta tsagaita wuta, wanda ya kawo ƙarshen yaƙin watanni 15 a zirin.

 Hamas ta bayyana yarjejeniyar a matsayin nasara ga juriya da gwagwarmayar Palasdinawa, tana mai cewa hakan wata babbar nasara ce wajen cimma ’yanci da dawowa.

Hamas ta godewa masu shiga tsakani daga Qatar da Masar, da kuma goyon bayan da abokan tarayya daga kasashen Larabawa, Musulmi, da na duniya suka bayar.

Kungiyoyi irin su Islamic Jihad da PFLP sun yaba da ƙoƙarin gwagwarmayar Palasdinawa tare da tunawa da shahidan da suka bayar da gudunmawa wajen cimma wannan nasara.

Hakanan kuma Shugabanni daga Yaman, Lebanon, da Iraqi sun taya Palasdinawa murna, suna masu jaddada muhimmancin tallafawa Gaza a matsayin nauyin addini da na ɗan adam.

Post a Comment

Previous Post Next Post