Sama da Sojojin Isra'ila 100 ne Aka Kashe a Iyakar Lebanon

 


Tun bayan fara arangama da ake yi a iyakar Lebanon, rahotanni daga Al Mayadeen sun tabbatar da cewa fiye da sojojin Isra'ila 100 ne suka rasa rayukansu yayin yunkurin su na kutsawa kudancin Lebanon.


A ranar 25 ga watan Oktoba, Ma’aikatar Tsaron Isra’ila ta tabbatar da asarar rayukan sojoji da jami’an tsaro 890 tun bayan fara Harin Ambaliyar al-Aqsa a ranar 7 ga Oktoba shekarar da ta gabata. Wannan sanarwa ta zama abin lura kasancewar Isra’ila na rufe gaskiya game da hasarar da ta ke fuskanta.


Bayanin ya nuna cewa daga cikin wadanda aka kashe akwai sojoji maza 835 da kuma mata 55. Haka kuma, cikin wadanda aka kashe akwai kwamandoji guda shida masu mukamin Colonel, wanda uku daga cikinsu sun mutu a ran 7 ga Oktoba a zafafan hare-hare. 


A cikin wadanda suka mutu akwai manyan sojoji 240 masu ajiye makami da kuma wasu sojoji 217 da ke aiki a wurare daban-daban. 


Muna Roqon Allah Daya qara ba Dakarun Musulunci Nasara.

Post a Comment

Previous Post Next Post