Dakarun Gwagwarmayar Musulunci a Iraki Sun Sake Kai Sabbin Hare Hare Kan Yankunan Da Aka Mamaye

 


Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci a Iraki ta sanar da kai hare-hare guda bakwai ta jiragen yaki masu nisan zango kan wuraren da Isra'ila ta mamaye a ranar Alhamis. Wadannan hare-hare sun yi nufin lalata manyan kayayyakin more rayuwa na Isra’ila da ke Golan da wasu sassa na arewa, tsakiya, da kuma kudancin yankunan da aka mamaye.


A yankin arewa, hare-hare guda biyu sun shafi al-Jalil, kuma a kudanci an kai harin jirage kan Umm al-Rashrash (Eilat), wanda ke bakin teku a Bahar Maliya. A tsakiya kuma, sauran hare-haren sun nufi wuraren tsaro na Isra'ila masu matukar muhimmanci.


Bayan kai wannan hari, mayakan Iraki sun sake sanar da wasu karin hare-hare guda biyar a ranar Juma’a, ciki har da guda uku a kudancin yankin da aka mamaye na Falasdinu, da kuma guda biyu a Golan. Sun sha alwashin ci gaba da kai hare-haren a matsayin goyon baya ga Falasdinu da Lebanon.

Post a Comment

Previous Post Next Post