Dakin Kai Hare haren Gwagwarmaya Musulunci na Hezbullah sun saki cikakken rahoto kan nasarorin da aka samu a gwabzawar da ake yi da sojojin mamaya na Isra'ila. Tun bayan fara yunkurin Isra'ila na kutsa kai cikin Lebanon, an kashe fiye da manyan jami’ai da sojoji 95 na Isra’ila, tare da raunata wasu fiye da 900.
A cikin nasarorin, Gwagwarmayar ta lalata manyan tankokin yakin Merkava guda 42, manyan motoci masu aiki guda hudu, Humvee guda biyu, wata motar yaki, da kuma motar daukar sojoji. Haka kuma, sun harbo jiragen leken asiri na Hermes 450 guda uku da Hermes 900 guda biyu.
Gwagwarmayar ta kara da cewa wannan kididdiga bata hada da asarar da Isra'ila ta yi a sansanonin soji, gidajen sojoji, gidaje, da kuma biranen da Hezbollah ke kaiwa harin rokoki mai karfi ba.
.jpeg)