A wani sabon rahoto daga dakarun mamayar Isra'ila, an bayyana cewa hafsoshi guda hudu sun rasa rayukansu yayin da wasu guda shida suka jikkata sosai a ci gaba da gumurzun da suke yi da mayakan Hezbollah a iyakar Lebanon da Falasdinawa.
Wani binciken farko na dakarun Isra'ila (IOF) ya nuna cewa wasu daga cikin mayakan Hezbollah sun fito ne daga wani rami, inda suka jefa wa dakarun Isra'ila bama-bamai, wanda hakan ya haifar da barna a sansanin sojojin na Isra’ila.
A yammacin ranar Laraba, dakin kai hare hare na gwagwarmayar Hezbollah ya fitar da takaitaccen rahoto game da halin da ake ciki a arangamar da ke gudana tsakanin dakarunsu da na Isra’ila a kudancin Lebanon, kusa da iyakar Falasdinu da aka mamaye.
Bisa sanarwar da Dakin kai hare-hare na Dakarun Hezbollah, sun ce Isra’ila ta tafka asarar rayukan sojoji sama da 70 tare da raunata wasu fiye da 600 daga cikinsu.
Muna roqon Allah ta'ala ya cigaba da ba Dakarun Musulunci Nasara akan Makiya Allah.


