A kwanan nan, Sashen Yada Labarai na Dakarun Gwagwarmayar Musulunci a Lebanon suka bayyana sabon makami da suka ƙera a cikin gida mai suna M-80. Wannan makamin harba rokoki wato "Rocket launcher" shine aka yi amfani dashi wajen kai farmaki kan sansanin sojan ruwa na Ras al-Naqoura a ranar 18 ga Oktoba.
M-80 tana zuwa ne a nau'i ka biyu, akwai tafi-da-gidanka da kuma na ajiyewa a wuri guda. Tana da ramuka guda 24 da ake saka harsasan Rokokin da za'a harba. Wannan fasalin yana ba ta damar kai hare-hare masu yawa a lokaci guda. Wannan ya sa ta zama kayan aiki mai amfani sosai a fagen fama.
Kowane harsashin rokar M-80 yana da diamita 80 mm, tsawon 95 cm, kuma nauyinsa kilo 10. Ko da yake wannan rokar ba ta da girman da ya kai na manyan makamai, tana ɗauke da ƙwallayen ƙarfe har guda 4,750 a kowanne harsashi. Wannan yana haifar da mummunar fantsama mai ƙarfi, wacce ke iya hallaka abokan gaba a cikin radius na mita 35.
An ƙera rokar M-80 don ta yi babban illa ga abokan gaba, tana iya kai hari da lalata sojojin da ke nisan har zuwa kilomita 3.3 daga wurin da aka kaddamar da ita. Wannan yana ba wa mayakan Juriya damar samun ƙarin goyon bayan wuta, wanda zai kara musu ƙarfin kariya da tasiri a filin daga.
