Ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hezbollah da ke Lebanon ta yi gagarumin harin makamai masu linzami kan yankin da aka mamaye a matsayin martani kan hare haren da gwamnatin mamaya ta Isra'ila ke kaiwa kan Lebanon.
A wata sanarwa da Hezbollah ta fitar a ranar Lahadi, ta ce mayaƙanta sun kai "gagarumin harin roka" zuwa sansanin sojojin Isra'ila da ke arewacin garin Safed da aka mamaye.
Ƙungiyar ta ce wannan harin na "kare Lebanon ne" kuma martani ne ga hare-haren da Isra'ila ke kaiwa kan birane, ƙauyuka da kuma fararen hula a Lebanon.
A nata ɓangaren, rundunar sojojin Isra'ila ta ce an harba akalla rokoki 70 daga Lebanon zuwa yankunan da ke arewa da aka mamaye a cikin 'yan mintuna kaɗan.
Bayan karar rawar gargadi da aka ji tsakanin 11:09 da 11:12 na safe a yankin Galilee ta Yamma da Upper Galilee, an gano kusan makamai 70 suna saukowa daga Lebanon, in ji sojojin Isra'ila.
Sabbin hare-haren na Hezbollah sun biyo bayan harin da sojojin Isra'ila suka kai a kudancin birnin Beirut, babban birnin Lebanon, a safiyar ranar Lahadi, inda suka ce sun yi niyyar kai farmaki kan hedikwatar leƙen asirin Hezbollah, saidai mazauna yankin sun ce duk hare haren nasu sun kai sune kan gidajen fararen hula.
Tun daga watan Oktoban 2023, Isra'ila ke kai hare-hare kan Lebanon, bayan ta ƙaddamar da yaƙi kan zirin Gaza.
Tun daga ƙarshen watan Satumba, Isra'ila ta ƙara ƙaimi a hare-harenta kan Hezbollah, har ta kai ga kashe shugabanta Sayyed Hassan Nasrallah da wasu manyan shugabannin ƙungiyar.
Aƙalla mutum 2,350 ne aka kashe da harin Isra'ila, kuma 10,906 ne suka Jikkata tun bayan fara hare haren a bara, a cewar ma’aikatar lafiya.
Ƙungiyar Hezbollah ta rantse za ta cigaba da kai hare-hare kan Isra'ila muddin gwamnatin mamayar ta cigaba da yaƙinta kan Gaza, wanda ya zuwa yanzu ya kashe aƙalla Falasɗinawa 42,519, mafi yawansu mata da yara.
