Rahotanni daga kafofin watsa labarai na Isra'ila sun bayyana cewa an kashe kwamandan Rundunar 401, wani babban kolonel a sojojin mamayar Isra'ila, yayin gwabzawa a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza.
Rahotannin sun nuna cewa wannan kwamandan ya rasa ransa ne sakamakon fashewar wata na'ura da aka girke a lokacin fadan. Wannan harin ya kuma raunata wasu jami'an soja na Isra'ila da dama.
A cewar kafofin watsa labarai, wannan kwamandan na Rundunar 401 yana daya daga cikin manyan jami'an sojan Isra'ila da aka kashe tun farkon mamayar kasa da suka kai a yankin Gaza. Wannan ya jawo hankalin duniya kan yadda yakin ya ƙara tsananta a yankin.
Tun bayan fara yaƙin kisan kare dangi a Gaza an kashe Falasɗinawa sama da 42,000 tare da Jikkata Sama da 90,000 wanda galibin su mata ne da kananan yara.
