Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci a Iraqi ta kai hari kan wani sansanin soji a ƙasar Falasɗinu da ke ƙarƙashin mamayar Isra’ila ta hanyar amfani da Jirage marasa matuka.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, ‘Yan Gwagwarmayar Musulunci a Iraqi sun bayyana cewa: “A cigaba da gwagwarmayar mu ta yakar mamaya, tare da goyon bayan mutanenmu a Falasɗinu da Lebanon, da kuma mayar da martani kan kisan kiyashin da ƙasƙantacciyar Ƙasa take yi wa fararen hula, ciki har da yara, mata, da tsofaffi, Mujahidan Gwagwarmayar Musulunci a Iraqi sun kai hari kan wani sansanin soji a ƙasar Falasɗinu dake ƙarƙashin mamaya, ta hanyar amfani da Jirage Marasa Matuka."
