'Yar Mamaya "Isra'ila" ta tabbatar da mutuwar sojoji biyar daga rundunar 'Golani' a Yammacin Ranar Alhamis, a yayin wani artabu mai tsanani a kudancin Lebanon, inda dakarun Gwagwarmayar Musulunci na Hezbollah suka ci gaba da jawa 'Isra'ila asarar manyan sojoji.
Kafofin watsa labarai na 'Isra'ila sun bayar da rahoton cewa mayakan Hezbollah hudu sun kai wa sojojin rundunar Golani hari a wuri mafi kusa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji biyar da jikkatar wasu biyar, inda uku daga cikinsu suka ji raunuka masu tsanani.
Daga cikin sojojin biyar da aka kashe akwai kwamandan kamfani (Company Commander), kwamandan tawaga, da kuma kwamandan ma'aikata daga rundunar 'Golani', kamar yadda su da kansu sojojin 'Isra'ilan suka amince.
A nasu bangaren, tashar talabijin ta 'Isra'ila Channel 12 ta ruwaito cewa an samu wani "mummunan lamari" a kudancin Lebanon, wanda ya haifar da jikkatar wasu karin sojoji guda tara.
A cikin cikakken bayaninsu, sojojin 'Isra'ila sun ce dakarun Golani sun shiga wani gini a ranar Laraba da taimakon sojojin sama. Bayan shigar sune, mayakan Hezbollah suka bude musu wuta a wani tsari mai kyau da suka kulla.
A lokaci guda, shafin intanet na 'Isra'ila Walla! ya ruwaito a baya cewa harin drone mai daidaito na Hezbollah a cikin dakin cin abincin rundunar 'Golani' da ke yankin 'Binyamina' daya yi sanadiyyar mutuwar sojoji hudu da jikkatar fiye da 60, ya girgiza 'Isra'ila tare da razana manyan kwamandojin sojojin 'Isra'ila gaba ɗaya.
"Lamarin da ya faru a sansanin rundunar Golani a kudu da Haifa ya tabbatar da gazawar tsarin tsaron 'Isra'ila wajen fuskantar hare-haren drone," kamar yadda shafin ya yi hasashe.
Haka nan, jaridar 'Isra'ila 'Maariv' ta bayyana harin a baya a matsayin wani mummunan lamari mai matukar tayar da hankali da ke da illa sosai ga rundunar mamayar, tana mai jaddada cewa 'Isra'ila ba ta da tsarin hana hare-haren drone da ake harbowa daga Lebanon, Gaza, Syria, Iraq, Iran da Yemen a halin yanzu.
