Aƙalla sojojin 'Isra'ila' guda bakwai aka ruwaito sun mutu yayin wata musayar wuta tsakanin rundunar Hezbollah ta ƙasar Lebanon da sojojin 'Isra'ila' a yankin iyakar kudu na ƙasar da yankunan Falasɗinawa da aka mamaye.
Kafofin watsa labaran 'Isra'ila' sun bayyana cewa an samu waɗannan asarar rayuka a yayin gumurzun daya faru a kusa da ƙauyukan Aita al-Shaab da Ramyeh da ke iyakar Lebanon a ranar Laraba.
Bugu da ƙari, an raunata wasu sojoji da dama, ciki har da wasu mutum 17 da suka ji munanan raunuka, yayin wata kwanton bauna da Hezbollah ta yi. Duk da haka, akwai rahotanni cewa Isra'ila ta dauki tsauraran matakai kan yaɗa lamarin.
Tun da farko, rahotanni sun nuna cewa aƙalla sojoji 49 da suka ji raunuka an kwashe su zuwa asibitoci a yankunan da aka mamaye na Falasɗinu bayan faruwar lamarin.
Daga cikin sojoji 49, sojoji 44 daga cikin su an kaisu zuwa asibitoci da ke cikin birnin Haifa, yankin arewa na ƙasar.
Asibitin "Rambam" da ke birnin ya bayyana faruwar taron gaggawa na masu raunuka, inda aka kira ƙarin ma'aikatan lafiya bayan jirage marasa matuƙi guda takwas suka sauka a wurin tare da waɗanda suka jikkata.
