Hezbollah Ta Kai Sabbin Hare-Hare Guda Biyar Kan Gwamnatin Sahyoniya

 


Ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hezbollah ta Lebanon ta sanar da kaddamar da hare-hare guda biyar kan sansanonin sojojin Isra'ila da ke arewacin Falasdinu da aka mamaye.


A cikin wata sanarwa, ƙungiyar Hezbollah ta bayyana cewa hare-haren sun kasance ne don tallafawa ƙasar Falasɗinu da gwagwarmayar jarumawan da ke fafutukar kare kasarsu, tare da kare mutanen Lebanon daga hare-haren Isra'ila da ake kaiwa kan birane, kauyuka, da fararen hula. 


Daga cikin wuraren da Hezbullah ta kaiwa hari har da sansanin sojojin "al-Baghdadi".


Sannan, an kai hari da makamai masu linzami biyu kan sojojin Isra'ila a sansanin Al-Marj, tare da wani harin makami kan yankin Khale Verde, wanda ke kusa da iyakar Lebanon da Falasdinu da aka mamaye, da kuma hare hare kan wuraren sojojin abokan gaba a Sadhana da ke yankin Shebaa Farms da aka mamaye a ranar Talata.


Rahotanni daga al-Mayadeen sun bayyana cewa an ji karar ƙararrawa a yankunan arewacin Falasdinu da aka mamaye.


A ranar 23 ga Satumba, sojojin gwamnatin Yahudawa sun kaddamar da wani gagarumin hari kan kudancin Lebanon. A cewar Ma’aikatar Lafiyar Lebanon, hare-haren sun hallaka daruruwan mutane tare da jikkata dubban su. Bayan kwana biyar, Hezbollah ta sanar da shahadar Shugaba Sayyed Hassan Nasrallah sakamakon gagarumin harin Isra'ila a kudancin Beirut. 


A matsayin ramuwar gayya, Hezbollah ta kaddamar da hare-hare masu yawa kan sansanonin sojojin Isra'ila da yankunan mazauna a arewacin Falasdinu da aka mamaye.


Bugu da ƙari, wasu majiyoyi sun bayyana cewa ƙungiyar gwagwarmaya musulunci ta Hezbollah ta harba makamai masu linzami biyu zuwa Haifa dake yankunan Falasɗinawa da aka mamaye.

Post a Comment

Previous Post Next Post