Kungiyoyin Gwagwarmayar Musulunci na Falasdinu Sun yi Nasarar Tarwatsa Tankokin Merkava Na Isra'ila Guda Biyu


 Kungiyoyin gwagwarmaya a Gaza sun samu gagarumar nasara a wani harin martani da suka kai kan rundunar sojojin mamayar Isra'ila, inda suka lalata tankokin yakin Merkava guda biyu a arewacin yankin Gaza.


A cewar Arabic 21, rundunar Saraya Al-Quds, reshen soja na ƙungiyar Islamic Jihad, ta bayyana cewa sun lalata daya daga cikin tankokin sojojin mamayar a tsakiyar sansanin Jabalia ta hanyar amfani da bama-baman Saqib.


Haka zalika, Bataliyoyin Ezzeddin al-Qassam, reshen soja na ƙungiyar Hamas, sun tabbatar da lalata wata Tanka ta Merkava a kusa da yankin al-Khazendar da ke arewa maso yammacin birnin Gaza.


Bataliyoyin al-Qassam sun kuma bayyana cewa sun kai wani hari na haɗin gwiwa a kudancin garin Shujaiyeh da ke birnin Gaza, inda suka jefa bama-bamai kan wuraren da sojojin mamayar suka mamaye.


Saraya al-Quds ta ƙara da cewa ta kai hari a wasu wuraren mamayar da ke kan layin agaji a ɓangaren Netsarim a tsakiyar Gaza. Wannan harin na nuni da ƙwazon ƙungiyoyin gwagwarmaya wajen tsayawa tsayin daka don kare yankin Gaza daga mamayar Isra’ila.

Post a Comment

Previous Post Next Post