Sama da Sojoji 50,000 na Isra'ila Sun Gaza Kama Ko Ƙauye Guda a Kudancin Lebanon

 


Jaridar Isra'ila Yedioth Ahronoth ta ruwaito cewa duk da Isra’ila ta tura sojoji sama da 50,000 daga rundunoni biyar — wato sojoji sau uku fiye da na yakin 2006 — sojojin mamayar Isra'ila ba su iya “kwace ko kauye guda ba” ko kuma samun wani mataki mai karfi a Kudancin Lebanon.


Rahoton ya danganta hakan da “ingantaccen dabarun yaki” na Hezbollah, da kuma matsalolin da sojojin Isra’ila ke fuskanta wajen gano wuraren Hezbollah da kuma dakile kananan jirage marasa matuki da suke gujewa ganowa.


Da yake tsokaci kan dabarun 'yan gwagwarmaya, Kanar Jack Neriya, tsohon mai ba Firayim Ministan Isra'ila Yitzhak Rabin shawara, ya bayyana cewa mayakan na Hezbollah suna barin sojojin mamayar Isra’ila su ci gaba da shigowa kafin su kulle su a cikin tarkunan da aka shirya da kyau.


Neriya ya kara da cewa, wannan dabara ta zama kalubale ga rundunonin sojoji na musamman na Isra’ila, ciki har da Rundunar Golani, kuma tana iya haifar da yawan asarar rayukan sojojin Isra'ila fiye da duk wani yaki tun daga karshen shekarun 1940.

Post a Comment

Previous Post Next Post