Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa zargin da ke cewa kasar Iran na kokarin kashe jami’an Amurka wani shiri ne da ‘yan mamayar Sahayoniyawa suka kitsa.
Esmaeil Baghaei Hamaneh ya bayyana cewa sake bayyana irin wadannan zarge-zarge a wannan lokaci wani "tsarin kazanta" ne domin ƙara tsaurara yanayin da ake ciki tsakanin Iran da Amurka.
A cikin jawabinsa, ya musanta wannan zargi yana mai cewa "bai da tushe ko asali" kwata-kwata.
Ya jaddada cewa an taba fitar da irin wadannan zarge-zarge a baya kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma a karshe an tabbatar da rashin gaskiyarsu.
Haka kuma, ya kara da cewa Iran za ta ci gaba da amfani da duk wasu hanyoyi na doka da suka dace wajen kare hakkin al'ummar kasar.
A ranar Jumma’a, kamfanin dillancin labarai na Amurka, Associated Press (AP), ya bayar da rahoto cewa ma’aikatar shari’ar Amurka ta bayyana wani shirin kisan kai da ake zargin wani dan Iran ne ya shirya domin kashe tsohon shugaban Amurka, Donald Trump. Rahoton ya nuna cewa wanda ake tuhuma ya ce an umarce shi daga wani jami'in gwamnati da ya tsara kisan kafin zaben wannan mako.
Masu fadi a ji na Amurka sun ci gaba da yada labarai marasa tushe kan Iran ta hanyar kirkirar tsare-tsaren da suke kira Iranophobia, suna zargin kasar da yunkurin kashe tsofaffin da sabbin jami’an Amurka, ciki har da Trump.
