Ƙungiyar gwagwarmaya ta Hezbollah daga Lebanon ta saki wani bidiyo mai mahimmanci da jiragen ta Marasa Matuka (Drone) suka ɗauka daga tsakiyar yankunan da Isra’ila ta mamaye na Filasɗinu. Wannan bidiyo ya kasance wani ɓangare na jerin bidiyoyin da ƙungiyar ke fitarwa tun watan Yuni da sukewa taken “Ga abinda Hoopoe ya dawo da shi.”
A ranar Laraba, Hezbollah ta saki wani sabon bidiyo wanda ya nuna cikakken hoto na yankin Haifa-Carmel, wanda yake da muhimmanci sosai ga tsaron yankin Tel Aviv. Wannan wuri yana ɗauke da wasu manyan wuraren sojan Isra’ila, ciki har da wurin da aka kafa na’urar Iron Dome, wanda ke taka rawa wajen tsaron Isra'ila daga hare-haren makamai masu linzami.
Bidiyon ya kuma nuna wasu manyan sansanonin sojan Isra'ila kamar sansanin Ramat David da ke kudancin Haifa, wanda yake da muhimmanci wajen sadarwa tsakanin hedikwatar sojan Isra'ila da ma'aikatar tsaronsu. Haka kuma, an nuna sansanin Mishmar HaCarmel da ke kula da tsaron yankin Haifa, da sansanin Ze'ev mai dauke da makaman David’s Sling, da sansanin Stella Maris wanda ke da na’urorin tsaron sararin samaniya.
Baya ga wannan, bidiyon ya kuma ratsa wasu manyan garuruwa kamar Nahariyya, Afula, Safad, da Kiryat Shmona, har ma da Golan Heights da Isra'ila ta mamaye daga Syria.
Hezbollah ta fara ɗaukan irin waɗannan bidiyoyi domin lura da motsin sojojin Isra’ila, wanda tun watan Oktoba suke ƙara kai hare-hare a Lebanon, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane a ƙasar. Ƙungiyar Hezbollah tana mayar da martani ga waɗannan hare-hare ta hanyar kai farmaki kan sojojin Isra’ila.
Haka zalika, a ranar Litinin, sojojin Isra'ila sun amince cewa a cikin sa'o'i 24 kacal, an jikkata sojojin su guda 38 a yayin wata arangama mai tsanani da Hezbollah a iyakar Lebanon. Wannan rikici ya hada da harin fiye da makamai 300 da Hezbollah ta kai musu yayin da sojojin suke ƙoƙarin kutsawa garin Mays al-Jabal. Hakanan, Hezbollah ta kai harin jirgin dron kan wata ƙungiyar sojojin Isra'ila da suke ƙoƙarin kutsa wa ta wurin Ras al-Naqoura.
