Isra’ila Ta Kulle Ɗan Jaridar Da Ya Bayyana Lalacewar Sansanonin Soja Da Iran Ta Kai Wa Hari

 


Hukumomin Isra’ila sun kama wani ɗan jarida mai bincike, Jeremy Loffredo, wanda ya fitar da wani babban rahoto da ya bayyana irin lalacewar sansanonin sojan Isra’ila da makamai masu linzami na Iran suka yi wa illa a makon da ya gabata.


A ƙarshen makon da ya wuce, Loffredo ya fitar da wani bidiyo a tashar YouTube mai suna The Grayzone, wata jarida mai zaman kanta daga Amurka. A cikin rahoton, ya nuna cewa hukumomin Isra’ila sun yi ƙoƙarin ɓoye girman asarar da sansanonin sojan su suka yi bayan hare-haren da Iran ta kai a lokacin Operation True Promise II.


A ranar 1 ga Oktoba, Sojojin Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) sun harba ɗaruruwan makamai masu linzami zuwa sansanonin soja, dana leƙen asiri a faɗin yankunan da Isra’ila ta mamaye.


Har zuwa yanzu, Isra’ila ta rufe gaskiyar yadda hare-haren suka yi barazana ga sansanonin su. Wannan aiki na Iran ya kasance martani ne ga kisan da Isra’ila ta yi wa shugabannin yankin, ciki har da shugaban Hamas, Ismail Haniyeh, a Tehran, da Sayyed Hassan Nasrallah na Hezbollah da kuma Abbas Nilforoushan, babban jami’in IRGC a Lebanon.


Jeremy Loffredo, ɗan jarida mai zaman kansa daga New York City, ya ziyarci wuraren da aka kai wa hare-hare domin tattara bayanai. Ya gano wasu wuraren da aka kai wa hari kusa da hedikwatar Mossad a Tel Aviv, wanda Isra'ila ba ta fitar da bayanai akansa ba. A ranar Laraba, Max Blumenthal, edita na Grayzone, ya sanar a shafinsa na X (Twitter) cewa Loffredo yana cikin ‘yan jaridar da sojojin Isra’ila suka kama. An kwace wayarsa kuma har yanzu yana tsare.


Wani ɗan jarida mai zaman kansa daga Rasha, Andrey X, ya bayyana cewa an buge shi, an rufe masa idanu, sannan aka kai shi sansanin soja tare da wasu ‘yan jarida guda hudu. Ya ce an tsare su na tsawon awanni 11 ba tare da tuhuma ba, an kwace wayarsa, kuma ɗaya daga cikin ‘yan jaridar har yanzu yana hannun hukumomi.


Isra’ila ta ƙara tsananta matakin ta kan ‘yan jaridu, musamman ma ‘yan jaridun Falasɗinawa, tun bayan fara yakin Gaza a ranar 7 ga Oktoba, 2023. Kawo yanzu, Isra'ila ta kashe fiye da 'yan jarida 150, yayin da wasu da dama ake ci gaba da tsare su a gidajen yari.

Post a Comment

Previous Post Next Post