Lebanon na Fuskantar Mummunan Hali: Majalisar Dinkin Duniya

 


Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta bayyana cewa Lebanon na cikin mummunan hali, inda mutane 600,000 suka tsere daga gidajensu sakamakon yaƙin Kisan Kiyashin da Isra'ila ke yi. 


A wani taro da aka yi a ranar Laraba, Jeanine Hennis-Plasschaert, mai kula da harkokin Lebanon a MDD, ta jaddada cewa ana ci gaba da kai hare-hare a kudancin Beirut, yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da kai farmaki a cikin kasar.


Hennis-Plasschaert ta ce, “Lebanon na fuskantar rikici da mummunan matsala ta rashin jin kai.” Ta yi nuni da cewa, sojojin Isra'ila suna ikirarin suna yaki da 'yan kungiyar Hezbollah ta Lebanon, yayin da suke ta ƙara kai hare-hare.


A cikin shekara guda da ta gabata, sama da mutane 2,000 sun mutu a harin Isra'ila, inda aka kiyasta cewa kusan miliyan daya sun tsere daga gidajensu, ciki har da mutane 400,000 da suka gudu zuwa kasar Syria.


Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya yi gargadi cewa Lebanon na iya fuskantar “yaƙi mai tsawo” kamar yadda aka gani a Gaza. 


Imran Riza, mai kula da jin kai a Lebanon, ya bayyana cewa Lebanon na fuskantar “daya daga cikin lokuta masu hadari na kisan gilla” a tarihin ta. Ya kuma bayyana cewa daga cikin waɗanda suka tsere, fiye da mutum 350,000 yara ne.


Hezbollah na yaki da Isra'ila tun daga ranar 8 ga Oktoba na shekarar da ta gabata, biyo bayan hare-haren da aka kai wa yankin Gaza. Kungiyar ta bayyana cewa za ta daina kai hare hare zuwa Isra'ila ne kawai idan Isra'ilar ta daina mamayar Gaza.October 4, 2024

Post a Comment

Previous Post Next Post