A wani mummunan hari da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon, mutane goma sun rasa rayukansu, ciki har da ma’aikatan lafiya biyar na agajin gaggawa. Wannan harin ta kai shine a cibiyar su dake Derdghaya a gundumar Tyre a ranar Laraba.
Ma’aikatan lafiyan na Lebanon suna kan aiki ne a cibiyarsu, suna jiran kira don taimakon gaggawa lokacin da Isra’ilar ta kai musu hari ta sama, wanda ya yi sanadin mutuwar su.
Wannan harin ya janyo suka mai tsanani daga Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon, wacce ta bayyana hakan a shafinta na X cewa Isra’ila tana karya dokoki na kasa da kasa da na jin kai, ta hanyar kai hari kan ma’aikatan ceto da motar asibiti ba tare da la’akari da ka’idojin jin kai ba.
A garin Wardaniyeh da ke yankin Tyre, wani harin sama da Isra’ila ta kai ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da raunata wasu 12. Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta bayyana cewa ana ci gaba da tantance sauran gawawwaki ta hanyar gwajin DNA.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadi kan kashe ma’aikatan lafiya da Isra’ila ke yi a Lebanon, tana mai cewa a cikin shekara daya da ta gabata, ma’aikatan lafiya sama da 100 aka kashe, yawancinsu cikin makonni biyu da suka wuce.
A yayin da ake ci gaba da wannan rikici mai tsanani, Hezbollah ta bayyana cewa tana ci gaba da kare yankunanta daga harin Isra'ila. Isra’ila ta tabbatar da mutuwar wani soja daga cikin sojojinta a lokacin da aka gwabza da Hezbollah a kudancin Lebanon. Wannan soja shine na 12 da Isra'ila ta rasa tun bayan kaddamar da farmaki kan Hezbollah a ranar 30 ga watan Satumba.
A cikin shekarar da ta gabata, Lebanon ta fuskanci zubar jini da rikice-rikice, inda Isra’ila ta kashe sama da mutane 2,000 tare da tilasta wa mutane miliyan daya barin gidajensu, ciki har da 400,000 da suka tsere zuwa Siriya.
Isra’ila ta kaddamar da wannan hari ne a matsayin wani bangare na yakinta da Gaza wanda tun daga watan Oktoba na shekarar da ta gabata ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 42,000, yawancinsu mata da yara.
Isra’ila ta fara wannan hari ne a matsayin wani ɓangare na yaƙinta da Gaza, wanda aka fara tun watan Oktoban bara wanda yayi sanadin mutuwar mutane 42,000, yawancinsu mata da yara.
